19 Yuni 2026 - 11:12
Source: ABNA24
Pentagon Ta Buƙaci Ƙarin Kasafin Kuɗi Dala Biliyan 80 Don Yaƙin Da Ta Ke Yi Kan Iran

Ma'aikatar Tsaro ta Amurka ta gabatar da buƙatar kasafin kuɗi na dala biliyan 80 don biyan kuɗaɗen yaƙin da ta ke yi kan Iran da wasu wasu kuɗaɗe.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: jaridar Wall Street Journal, ta nakalto majiyoyin da suka san lamarin cewa "Steven Feinberg", mataimakin ministan yaƙi na Amurka, a cikin tuntuɓar waya da 'yan majalisar dokokin Amurka a wannan makon, ya sanar da cewa ma'aikatar tana buƙatar dala biliyan 80 don kuɗaɗen yaƙin da ake yi kan Iran tare da wasu makudan kuɗaɗen na daban.

Bisa ga rahoton jaridar "Al-Arabi Al-Jadeed", Wall Street Journal ta kara da cewa, buƙatar ƙarin kasafin kuɗi mai faɗi zai ƙunshi kudaden Pentagon da kuma abubuwan da suka shafi farar hula kamar taimakon noma da shirye-shiryen agaji akan wasu lamura da ka iya faruwa kwatsam, kuma ana iya gabatar da shi ga wakilan majalisar dokokin Amurka a kwanaki masu zuwa.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayyana cewa har yanzu bai sami damar tabbatar da wannan rahoton da kansa ba, kuma a wajen lokutan aiki na hukuma, Fadar White House ko Pentagon ba su bayar da wani ra'ayi game da wannan batu ba.

Kuɗin Dala Biliyan biliyan 25 A Ƙididdigar Farko 

Wani jami'in Pentagon a watan Afrilu da ya gabata ya shaida wa Reuters cewa, yaƙin da ake yi wa Iran ya ci kuɗi kusan dala biliyan 25 a yanzu.

Wannan adadi shi ne farkon ƙididdigar hukuma game da kuɗaɗen yaƙin da aka batar akan Iran. Duk da haka, kuɗin ƙarshe na yaƙin da Donald Trump, shugaban Amurka, ya fara tare da haɗin gwiwar sahayoniyar daga 9 ga watan Isfand, shekara1404, har yanzu yana cikin tafka mahawara da tambayoyi a majalisar dokokin Amurka.

Adawa Da Buƙatar Kasafin Kuɗi Na Dala Biliyan 200

Kafin wannan, an fuskanci buƙatar farko na dala biliyan 200 don samar da ƙarin kasafin kuɗi da adawa mai tsanani daga wasu 'yan majalisar dokokin Amurka.

A watan Afrilu, "Russell Vought", darektan ofishin gudanarwa da kasafin kuɗi na Fadar White House, a zaman sauraron kwamitin kasafin kuɗi na majalisar wakilan Amurka, ya bayyana cewa ba shi da wani ƙididdiga na kuɗaɗen yaƙin da ake yi wa Iran. Waɗannan kalamai sun zo ne a yayin da yake kare buƙatar Trump don amincewa da kasafin kuɗi na soji na shekara-shekara na dala tiriliyan 1.5

Damuwa Game Da da Kuɗaɗen Tattalin Arzikin Yaƙin Da Aka Yi Wa Iran

Kasafin kuɗin da aka ba da shawara, yana nuna fifikon jam'iyyar Republican kafin zaɓen tsakiyar wa'adi na Nuwamba mai zuwa. Zaben da jam'iyyar ke ƙoƙarin ci gaba da riƙe ikon majalisa.

An gabatar da wannan buƙatar a daidai lokacin da damuwar masu zaɓe na Amurka game da hauhawar kuɗaɗen rayuwa, farashin makamashi, da matsin kuɗi na yaƙin da ake yi wa Iran ya ke ƙaruwa.

........

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha